✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta haramta wa ’yan jarida halartar shari’ar Nnamdi Kanu da Boko Haram

Ba za a lamunci kowa ya shiga cikin kotun da wayoyin salula ko wasu na’urorin da ke iya nadan sauti ko bidiyo ba.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, ta haramta wa ’yan jarida da sauran jama’a halartar shari’ar Nnamdi Kanu da wadanda ake tuhuma da daukar nauyin ta’addancin Boko Haram.

Alkalin alkalan babbar kotun tarayyar, John Tsoho ne ya fitar da wata sanarwa da ke bayyana yadda kotun za ta rika gudanar da shari’un da suka jibanci ta’addanci a gaban kotun.

Daga cikin shari’un da ke gaban kotun, akwai wanda ake wa Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar masu fafutikar kafa yankin Biyafara ta IPOB da gwamnatin Najeriya ta ayyana a matsayin kungiyar ta’addanci da ta ’yan canjin kudi da ake tuhuma da taimaka wa ’yan ta’adda, da kuma mayakan Boko Haram.

Alkali Tsoho ya ce sababbin tsare tsaren gudanar da ayyukan kotun na karkashin dokar kasa da ke kunshe cikin sashe na 254 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.

Sanarwar ta ce a karkashin wannan sabon tsarin, za a hana kafafen yada labarai halarta da daukar rahotanni kan shari’un, sai dai idan kotun ta amince da haka.

Kotun ta kuma bayyana cewa za a rika gudanar da wasu shari’un ta hanyar amfani da fasahar zamani wato ta amfani da bidiyo da kuma ta kafar sadarwa ta intanet.

Baya ga ’yan jarida, za a kuma hana sauran jama’a halartar shari’un, in dai ba wanda ake tuhuma da aikata laifukan ta’addanci ba da kuma lauyoyinsu.

Sannan sanarwar ta ce ba za a lamunci kowa ya shiga cikin kotun da wayoyin salula ko ma wasu na’urorin da ke iya nadan sauti ko bidiyo ba yayin da ake zaman shari’ar ba.

A karshe sanarwar ta yi gargadin cewa za a hukunta duk wanda ya karya wannan sabon tsarin karkashin sashe na 34(5) na dokar da ke hukunta laifukan ta’addanci ta 2011.