Babbar Kotun Jihar Legas ta bai wa jm’iyyar LP da magoya bayanta umarnin kada su kuskura su gudanar da gangamin siyasa a ‘tol get’ din Lekki da ke jihar.
Kotun, wacce ke karkashin Mai Shari’a Daniel Osiagor, ta hana gangamin ne mai taken #ObiDatti23 Forward Ever Rally’ wanda magoya bayan dan takarar jam’iyyar, Peter Obi suka shirya gudanarwar ranar daya ga Oktoba, 2022.
- Kotu ta daure basaraken da ya yi garkuwa da kansa shekara 15
- ‘Masu rayuwa a karkashin turakun lantarki za su iya fuskantar rashin haihuwa’
Sai dai kotun ta ce ba ta hana magoya bayan gudanar da gangaminsu a sauran wurare hudun da suka shirya yin hakan a jihar ba.
Duk da umarnin hanin, kotun ta ce babu laifi masu gangamin na iya shigewa ta tol get su wuce zuwa sauran wurare, amma babu tsayawa ko hada taro a wajen.
Tol get din na Lekki dai na dada samun tagomashi ne tun bayan hargitsin da ya auku lokacin zanga-zangar #EndSARS a watan Oktoban 2020.
Lamarin da ya kai ga asarar rayuka wanda ya yi sanadiyar rufe kofar na wani lokaci.