✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta hana INEC tuhumar Hudu Ari

Lauyan A'isha Binani ne ya shigar da INEC karar

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Litinin ta dakatar da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) daga tuhumar dakataccen Kwamishinan Zaben Jihar Adamawa, Barista Hudu Ari a gaba kotu.

A makon da ya gabata ne dai INEC ta ayyana yunkurin da ta ce tana yi na gurfanar da Malam Hudu a kotu, saboda bayyana sakamakon zaben Gwamnan Adamawa tun kafin a kammala tattara sakamakonsa.

A watan Afrilu din da ya gabata ne Hudu ya ayyana sunan Aishatu Dahiru Binani ta jam’iyyar APC a matsayin wacce ta lashe zaben, kafin daga bisani INEC ta soke sanarwar.

To sai dai a ranar Litinin, alkalin kotun, Mai Shari’a Donatus Okonkwo, ya bayar da umarnin, bayan lauyan Aisha Binani ya bukaci hakan.

A kwafin karar mai lamba: FHC/ABJ/CS/935/2023, ’yar takarar Gwamnan ta APC, ta maka INEC da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya.

Lauyan ya ce matakin da INEC ke shirin dauka na gurfanar da Hudu a gaban kotu kan ayyana Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaben a ranar 15 ga watan Afrilu, kafin kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke hukunci kan wacce yake karewa zai hana ta cin gajiyar sashen dokar da ya bayar da kwana 180 ga karar da aka shigar ranar 6 ga watan Mayu.

Bayan sauraron karar ta lauyan A’isha, wato Barista Aondoka, Mai Shari’a Okorowo, ya umarci wadanda ke cikin karar da kada su dauki wani mataki har zuwa lokacin da za a kammala sauraron karar.

Daga nan ne ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 18 ga watan Yulin 2023. (NAN)