Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bayar da umarnin wucin gadi na hana EFCC, kama tsohon Ministan Tsaro, Lawal Batagarawa, kan taƙaddamar fili.
Kotun ta kuma umarci EFCC da ta daina gayyatar Batagarawa ko tsoratar da shi yayin da ake ci gaba da sauraron shari’ar.
- Isra’ila ta ɗaiɗaita yara sama da 400,000 a Lebanon — UNICEF
- Ba zan ce uffan kan rikicin NNPP a Kano ba — Kwankwaso
Wannan umarni ya biyo bayan ƙorafin da Batagarawa ya shigar cewa EFCC tana ci gaba da damunsa kan batun filin.
Ya bayyana cewa an tsare shi na tsawon sa’o’i a ofishin EFCC kuma ya sha gayyata da kiran waya ana tsoratar da shi.
Lauyan Batagarawa, Jerry Aondo, ya shigar da ƙarar ne a kotu inda ya zargi EFCC da tauye haƙƙin wanda yake karewa.
Batagarawa, ya ce filin da ake rikici a kai Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya (FCDA) ce, ta ba shi a shekarar 2001.
Batagarawa ya gabatar da hujjar biyan kuɗin filin.
Amma EFCC ta yi iƙirarin cewa filin mallakinsu ne, wanda hakan ya jawo taƙaddama.
Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 31 ga watan Oktoba, 2024, inda za ta tattauna batun kare haƙƙin ɗan Adam game na Batagarawa.