Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta hana a binciki wani mutum da Hukumar EFCC ke zarginsa da almundahanar Naira miliyan 25, inda kotun ta ce wannan umurni nata zai ci gaba har sai an zo gabanta an tantance gaskiyar magana.
Tun da farko wadasu mutane ne daga kasar Kodibuwa suka kai karar mutumin mai suna Nasiru Tijjani gaban Hukumar EFCC, cewa sun ba shi Naira miliyan 25 don ya yi musu addu’a. Hakan ya sa jami’an hukumar suka kama shi, inda ya shafe kwana 50 a hannunsu da sunan bincike.
Wanda ake zargin ya musanta da’awar mutanen Kodibuwan, inda ya ce bai ma taba ganinsu ba, ballantana wata huldar kudi ta hada su.
Wanda ake zargin ya kuma nemi gwamnati ta sanya baki game da barazanar da jami’an Hukumar EFCC ke yi masa a kan batun. “Duk da cewar kotu ta bayar da wancan umarni amma har yanzu jami’an ba su kyale ni ba, domin sun ci gaba da yi mini barazana, suna haurawa gidana tare da cin mutuncin iyalina, yanzu haka daya daga cikin matana ba ta da lafiya sakamakon dukan da suka yi mata, duk a kan laifin da ba nawa ba. Don haka nake neman Gwamnan Jihar Kano da Mai martaba Sarkin Kano su shigo cikin lamarin,” inji Nasiru Tijjani.
Sai dai duk kokarin Aminiya na jin ta bakin Hukumar EFCC din abin ya ci tura, inda suka nuna cewa ba su da hurumin yin magana a kan batun sai dai a je Abuja.