✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta hana Aminu Bayero yi wa Fadar Nassarawa kwaskwarima

Kotun ta ce Kowane ɓangare ya dakatar har zuwa lokacin da za a yanke hukunci.

Babbar Kotun Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Dije Abdu Aboki, ta bayar da umarnin hana Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, yi wa ginin Fadar Nassarawa kwaskwarima.

Gwamnatin Jihar Kano, ta hannun Babban Lauyanta da kuma Masarautar Kano ne, suka maka Aminu Ado Bayero a kotu.

Kotun ta bayar da umarnin cewa dukkanin ɓangarorin da ke cikin wannan shari’a su bar komai yadda yake game da tsarin ginin fadar har sai an saurari ƙarar tare da yanke hukunci.

Umarnin kotun ya ce: “An bayar da umarnin wucin gadi na hana wanda ake ƙara, wakilansa, ko duk wanda ke aiki bisa umarninsa daga rushe, gyarawa, ko sake gina Gidan Sarki na Nassarawa da ke kan titin zuwa Gidan Gwamnatin Kano, har sai an saurari wannan ƙara tare da yanke hukunci.”

Takardun kotun wadda wakilinmu ya gani, ta nuna cewa masu ƙara sun shigar da ƙarar ne a ranar 9 ga watan Satumba.

Ƙarar mai sakin layi 33 da Matawallen Kano, Alhaji Ibrahim Ahmed, ya sanya wa hannu

Kotu ta kuma bayar da umarnin a kai wa Sarkin takardun kotu ta wata hanya ta daban, tare da tsayar da ranar 2 ga watan Oktoba domin sauraron ƙarar.