✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta fara karanta hukuncinta kan zaben Zaben Gwamnan Kaduna

An n kammala hada na'urorin da za a yi amfani da su a yayin zaman kotun ta Zoom

Kotun zaben Gwaman Jihar Kaduna ta fara sanar da hukuncinta kan shari’ar ta intanet, ta manhajar Zoom.

Kotu za ta yanke hukunci ne kan karar da babbar jam’iyyyar adawa ta PDP da dan takararta, Isah Muhammad Ashiru ne suka garzaya kotun suna kalubalantar nasarar Gwamnan Uba Sani na Jam’iyyar APC a zaben.

A yayin da bangarorin da ke shari’ar suke jiran kotun da ke zamanta a harabar Babbar Kotun Jihar Kaduna, ta sanar da hukuncin da yanke, kowanne bangare ya nuna kwarin gwiwar samun nasara a shari’ar.

Tun da farko wakiliyarnmu da ke can ta ruwaio cewa bisa dukkan alamu alkalan ba za su halarci zaman da kansu ba, za su yanke hukuncin ne ta intanet ta manhajar Zoom.

Tuni kuma aka kammala hada na’urorin da za a yi amfani da su a yayin zaman kotun ta Zoom, inda ake sa ran alkalan za su karanta hukuncin da suka yanke daga wani wuri.

A cikin garin Kaduna kuma, an tsaurara matakan tsaro domin tabbatar da doka da oda, a yayin da lauyoyi da bangarorin da da ke shari’ar suke jiran jin yadda za ta kaya.