✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnan Kano ya nada sabbin hadimai 94

Hadiman Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano sun doshi mutum 300, bayan ya nada karin wasu 94.

Adadin hadiman Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya karu zuwa mutum 290, inda ya nada sabbin hadimai 94 a bangaren aikin jarida.

Gwamnan ya nada karin ’yan jaridan ne a matsayin masu kawo rahoto da manyan masu kawo rahoto kan ayyukan hukumomi da ma’aikattun gwamantin jiar.

Sanarwar nade-naden da kakakinsa, Sanusi Bature, ya fitar ta ce hakan ya dace da tsarin gwamnatin na ba wa Kanawa bayanan ayyukan gwamantin, “da nufin samar da shugabanci mai inganci.

“Za a tura su zuwa hukumomi da ma’aikatu su rika kawo rahotanni da nufin tabbatar da gaskiya da yin komai a fiili a tafiyar da gwamanti da tsare-tsarenta,” in ji shi.

Da wannan nade-naden, gwamnan na da hadimai kuma wakilai biyu a kusan duk hukumoi da ma’aikatun gwamantin jihar, inda ya bukace su da su gudanar da aikinsu bisa kwarewa da kuma amfani da fasahar zamani.

%d bloggers like this: