✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure ’yan jaridar bogi a gidan yari a Kano

Kotun Shari’ar Musulunci a Jihar Kano ta yanke wa wasu ’yan jaridar bogi biyu hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari kan laifin damfarar ’yan…

Kotun Shari’ar Musulunci a Jihar Kano ta yanke wa wasu ’yan jaridar bogi biyu hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari kan laifin damfarar ’yan kasuwa ta hanyar tura musu sakon kudi na bogi.

Tunda farko an gurfanar da Abba Imam, mazaunin unguwar Zoo Road tare da Mujahid Kabir mazaunin Sultan Road ne kan zargin hada kai, aikata laifi da kuma yin sojan gona da cewar su ma’aikatan gidan Radiyon Vision ne.

Wani ma’aikacin gidan radiyon ne mai suna Sharif Ahmad ne ya kai wa ’yan sanda korafi cewa wadanda ake zargin sun je ofishinsu da nufin bayar da tallace-tallace, inda suka yi amfani da damar suka sace katin shaidar ma’aikatansu guda biyu.

Bayan sun tafi ne suka je aka yi musu irinsa na bogi mai dauke da sunayensu, suka rika amfani da su suna gabatar da kansu a matsayin ’yan jarida.

Dubun ’yan jaridar bogin ta cika ne a wani shago da suka sayi dardumar daki da kwamfuta da wayar hannu ta Naira dubu 90 suka tura ‘Alert’ na bogi.

Bayan ’yan jaridar bogin sun shiga hannu, ’yan sanda suka gurfanar da su a gaban kotun Shari’ar Musulinci da ke unguwar Kwana Hudu karkashin jagorancin Mai Shari’a Mallam Nura Yusuf.

A lokacin zaman kotun, mai gabatar da kara, Aliyu Abidin, ya karanto kunshin tuhumar da ake yi musu, kuma nan take  ’yan jaridar bogin suka amsa.

Daga nan mai gabatar da karar ya yi roko karkashin sashi na 356 karamin sashi na (2) ACGL, domin a hukunta su ba tare da bata lokaci ba, kuma kotun ta amsa rokonsa.

Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmad ya yanke wa wadanda aka gurfanar din da hukuncin daurin watanni 4 a gidan yari, sai kuma daurin wata 6 a kan laifi na biyu ba tare da zabin biyan tara ba.

Haka kuma kotun ta yi musu bulala 30 a laifi na uku sai kuma laifi da aka yi musu hudu daurin shekara daya ko zabin biyan tarar Naira dubu 30.

Kotun ta umarci wadanda aka yanke wa hukuncin, su biya ma’aikatan gidan Radiyon Vision Naira 15,000 na zirga-zirgar da suka yi tun daga lokacin da aka kama su har zuwa karshen shari’ar.