Wata Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Jihar Legas, ta yanke wa dan Majalisar Dattawa na jam’iyyar APC da ke wakiltar mazabar Delta ta Arewa, Sanata Peter Nwaoboshi, daurin shekara bakwai gidan yari.
Kotun ta kuma bayar da umarnin rufe kamfanoninsa biyu, Golden Touch Construction Project Ltd da Suiming Electrical Ltd, bisa tanadin sashe na 22 na Dokar Laifin halatta kudin haram ta Najeriya ta 2021.
- Kotu ta dakatar da Gwamnatin Kano daga karbo bashin Naira biliyan 10
- ’Yan bindiga sun kashe sojoji 22 da ‘yan sanda 7 a Neja da Taraba
Hukuncin kotun ya biyo bayan nasarar daukaka karar da ke kalubalantar hukuncin da Mai shari’a Chukwujekwu Aneke na Babbar Kotun Tarayya ya yi ne a ranar 18 ga watan Yuni, 2021, wanda ya wanke tare da sallamar wadanda aka tuhuma da laifin zamba da kuma halatta kudin haram.
Hukumar da ke yaki da rashawa ta EFCC ta cafke mutanen uku da ke da alaka da wannan batu kan zarginsu da mallaka kadarori a wasu yankunan uku da ke Apapa na Legas kan naira miliyan 805.
Amma alkalin kotun, Mai shari’a Aneke ta ce masu gabatar a kara sun gaza gabatar da shaidu masu karfi da hujojji kan tuhuma-tuhuman.