✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure wanda ya bata sunan Dagaci

A ranar Alhamis din makon jiya ne alkalin Kotun Shari’a ta daya da ke garin Kafanchan, Mai shari’a Shitu Umar, ya yanke wa Mista Bawa…

A ranar Alhamis din makon jiya ne alkalin Kotun Shari’a ta daya da ke garin Kafanchan, Mai shari’a Shitu Umar, ya yanke wa Mista Bawa Kantiyok hukuncin daurin wata tara ko ya biya tarar Naira dubu 40, saboda samunsa da laifin bata sunan wani dagaci mai suna Mista Joshua da dukkansu suka fito daga yankin Madakiya a karamar Hukumar Zangon Kataf a Kudancin Jihar Kaduna.
A lokacin da alkalin yake karanta hukuncin, ya ce bisa la’akari da shaidun wanda aka bata wa suna ya gabatar, tare da irin mutuncin da yake da shi, tanadi na 137 na dokokin shari’a, kotu ta ci yanke hukunci ga wanda ake kara ya biya Naira dubu 30 a matsayin diyya ga wanda ya bata wa suna, kuma ya biya tarar Naira dubu 10, ko kuma ya yi zaman kaso na wata tara. Shari’ar ta biyo bayan shigar da kara ne da Dagaci Joshua ya yi inda yake zargin Bawa Kantiyok da yi masa kazafin ya yi wa wata mace tsirara, ya kuma kwace mata riga da zani da takalmanta wanda hakan ya sa ta ruga tsirara zuwa wajen mijinta tana rokon ya yafe mata laifin da ta yi masa, zargin da matar da mijinta suka musanta.    
Alkalin ya ce ya zartar da wannan hukunci ne da fatan ya zama darasi ga duk wani mai kokarin bata wa wani suna nan gaba ta hanyar kazafi.