✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure sojojin da suka kashe mata da yara a Kamaru

Kotun Sojin kasar Kamaru ta yanke wa wasu sojojin kasar hudu hukuncin daurin shekara 10 a bayan ta same su da hannu a kisan wasu…

Kotun Sojin kasar Kamaru ta yanke wa wasu sojojin kasar hudu hukuncin daurin shekara 10 a bayan ta same su da hannu a kisan wasu kananan yara biyu da kuma wasu mata biyu a shekarar 2015

Kotun da ke zamanta a Yaounde, hedikwatar Kamaru ta kuma yanke wa wani soja hukuncin daurin shekaru biyu a yayin da ta wanke na bakwan wadanda aka gurfanar din.

Bidiyon abun da sojojin suka yi a 2015 ya karade kafafen sadarwa a 2018 ya nuna sojojin sun rufe wa matan fuska suka hahharbe su, bisa zarginsu da alaka da kungiyar Boko Haram.

Bidiyon ya nuna yadda aka harbe sojojin suka harbi matan sau 22 a gefen hanyan; cikin matan har da wata mai goyo.

Da farko gwamantin Kamaru ta yi watsi da bidiyon a matsayin na bogi.

Daga baya wani binciken kwakwaf na shirin BBC Africa Eye ya gano cewa an aikata kisan ne a wani kauye da ke yankin Arewa mai nisa na Kamaru.

Binciken kwakwaf din ya kuma gano tantance sojojin da suka kashe matan da kananan yaran.