Wata kotun majistare da ke Ibadan a Jihar Oyo ta tisa keyar wani mutum mai shekaru 23 gidan gyaran hali saboda satar jar miya a gidan abinci.
Mutumin, mai suna Isaac Dumabara zai shafe tsawon wata guda, bisa samunsa da laifin satar tukunyar jar miyar da ta kai darajar Naira dubu 40 a wani gidan sayar da abinci.
- Dalibin JSS1 ya kirkiro janaretan da ba ya amfani da fetur a Maiduguri
- NAJERIYA A YAU: ‘Yadda sojoji suka bindige kanina saboda fetur a Neja’
Alkalin kotun, Mai Shari’a S. A. Adesina ya tisa keyar mutumin zuwa gidan gyaran halin ne ba tare da zabin biyan tara ba.
Tun da fari dai lauyan da ke kara, ASP Sikiru Ibrahim ya shaida wa kotun cewa bayan satar tukunyar jar miyar, Damubara ya kuma dauke na’u’rar Stabileza.
Kazalika, ya ce mutumin ya saci takalmi kirar Adidas daga wani gidan abinci da ke titin Magara, a Iyaganku da ke jihar.