Kotun Majistare mai zamanta a Ikeja, Jihar Legas, ta daure wani matashi shekara hudu da rabi a gidan yari kan zargin satar kunzugun yara (pampers) wanda a kiyasce kudinsu ya kai Naira miliyan 13.5.
Ana tuhumar matashin da aikata laifuka uku da suka hada da hadin baki da sata da hana zaman lafiya.
- NAJERIYA A YAU: Kalubalen da muke fuskanta a harkar sufuri – ’Yan Najeriya
- Majalisa ta bukaci CBN ya kara wa’adin daina karbar tsoffin kudi
Alkalin Kotun, Lateef Owolabi, ya ce, “A wannan yanayi akwai bukar aika da sako mai karfi musamman ga mai kare kansa da ma al’umma.”
Ya fara ne da yanke wa matashin hukuncin zaman kurkuku na shekara guda ko biyan tarar N200,000 kan laifin hadin baki.
Sannan shekara uku a gidan yari ko biyan tarar N200,000 kan laifin sata, sai kuma wata shida a kurkuku ko biyan tarar N10,000 kan laifin hana zaman lafiya.
Kotu ta kuma bukaci mai kare kansa da ya maida kayan da ya sata din ga mai shi, Okuoromi Ehighamhe.
Owolabi ya ce yayin shari’ar, da fari mai laifin ya ki amsa tuhuma amma daga bisani ya amsa aikata laifin tare da rokon sassauci daga kotu.
Mai gabatar da kara, SP Josephine Ikhayere, ta fada wa kotun cewa a Agustan 2022 mai laifin ya hada baki da wasu wajen sace kaya, wanda hakan ya saba wa sassa na 411 da 173 da na 287 na Dokokin Haramta Manyan Laifuka na Jihar Legas na 2015.