Wata kotun Abuja mai zamanta a yankin Karu, ta daure matashi shekara uku a gidan yari kan laifin satar kayan kicin a Otel.
Sai dai Alkalin kotun, Umar Mayana, ya bai wa matashin zabin biyan tarar N100,000, kana ya gargade shi a kan ya guji aikta laifuka a nan gaba.
- Ko ta daure ‘yan fashin babur shekara 28 a kurkuku
- An ceto mata masu juna-biyu 10 daga masana’antar kyankyasar jarirai a Ribas
Mai laifin ya amsa tuhuma, ya kuma nemi kotun ta tausaya masa.
Tun da farko, lauya mai gabatar da kara, Mista Olarewaju Osho, ya fada wa kotun cewar an tsare tare da kai mai laifin ofishin ‘yan sandan Jikwoyi a ranar 28 Nuwamban 2022.
Ya ce yayin binciken ‘yan sanda, mai laifin ya amsa ya shiga “Bencalic Otel” inda ya sace wasu kayayyaki.
Laifin da lauyan ya ce hukuncinsa na karkashin sassa na 348 da 287 na ‘Penal Code’.
(NAN)