✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu Ta Daure Matashi Kan Satar Kaza a Kano

Wata kotun Majistare da ke Kano ta daure wani matashi da aka gurfanar bisa zargin sa da yunkurin satar kazar wani mutum.

Wata kotun Majistare da ke Kano ta daure wani matashi da aka gurfanar bisa zargin sa da yunkurin satar kazar wani mutum.

Kotutn ta kama matashin da laifin shiga gida ba da izini ba da kuma yunkurin yin sata, kuma ya amasa, tare da rokon alkali ya yi masa sassauci.

Alkalin kotun, Abdul’aziz Mahmud, ya yanke masa hukuncin daurin wata guda ko biyan tarar N5,000 da kuma sharadin cike takardar rantsuwar zama mutumin kirki a gaba.