An gurfanar da wani matashi a kotu kan sace kayan abinci a wani gida da kuma kone gidan a Jihar Kwara.
Hukumar tsaro ta Sibil Difens ta gurfanar da matashin ne kan sata da kayan gidan, inda alkali ya tusa ƙayarsa zuwa Gidan Yarin Mandala da ke jihar.
Mai Shari’a na kotun Majistaren ya yanke hukuncin daurin shekara guda ba tare da zaɓin biyan tara ne bayan da ya samu matashin da laifi.
A ranar 26vga watan Satumba 2024 ne matashin ya fasa gidan a cikin dare a yankin Onireke, Upper Gaa Akanbi, da ke Karamar Hukumar Ilorin ta Kudu.
Ya saace kayan abinci da kayan daƙi da sauransu, sannan ya Banks wa gidan wuta.
Ya banka wa gidan wuta ne a kokarinsa na tserewa bayan jama’a sun yi yunkurin kama shi.
Amma daga bisani an yi nasarar kama shi aka damƙa wa jami’an Sibil Difens.