Wata Kotun Majestare a Ota, Jihar Ogun, ta yanke wa wani matashi hukuncin zaman kurkuku na wata hudu kan laifin sata.
Kotu ta kama matashin ne da laifin satar kuloli da karafunan taga da gilasai wadanda darajarsu ta kai N200,000.
- An yi wa gwamnan Taraba ihun ‘ba mu so’ a wurin taro
- NAJERIYA A YAU: Yadda Likita 1 ke Duba Lafiyar Mutum 45,000 A Arewacin Najeriya
Ba tare da wahalar da kotun ba, matashin ya amsa laifinsa a gaban kuliya.
Da take yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai Shari’a A.O. Adeyemi ta daure matashin na wata hudu a gidan yari ba tare da wani zabi ba.
Tun farko, lauyan mai tuhuma, Sufeta E.O. Adaraloye, ya shaida wa kotun cewa matsahin ya aikata laifin da aka kama shi da shi ne a ranar 14 ga Oktoba a yankin Ota.
Laifin da a cewarsa, ya saba wa Sassa na 390(9) da 411(2) na Dokokin Manyan Laifuka na Kundin Dokokin jihar na 2006.