✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure mai walda saboda sata

Kotun Majistare da ke zama a Osogbo, Jihar Osun, ta yanke wa wani mai sana’ar walda hukuncin daurin wata shida a gidan yari kan satar…

Kotun Majistare da ke zama a Osogbo, Jihar Osun, ta yanke wa wani mai sana’ar walda hukuncin daurin wata shida a gidan yari kan satar kayan laturoni.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sifeto Adeoye Kayode ya fada kotu cewar da misalin 11:20 na daren ranar 18 ga watan Agusta, 2020, mai laifin ya yi aika aikan a titin Basi Bankole da ke Oke Onitea, a Osogbo.

Adwoye ya ce mutumin ya fasa shagon wani da ake kira Azeez Fatai, ya sace kan fankar sama, man mota, dutsin guga biyu lalatattu da koyal da kuma fankar kasa da darajarsu ta kai N60,000.

Ya ce, laifin da ya saba doka kuma za a hukunta shi karkashin sashe na 413 da 309 na dokar manyan laifuka ta Jihar Osun ta 2002.

Mai laifin, Kola Rasheed, wanda bai dauki lauyan da zai kare shi ba, bai musunta zargin da aka yi masa ba.

Sai dai ya ce makwabta sun doke shi suka kuma sace masa N2,500 da ke aljihusa kafin isowar ‘yan sanda.

A hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a Opeyemi Badmus, ya tura mai laifin gidan yari na wata shida ba tare da zabin tara ba.