Babar Kotun Jihar Kwara ta daure wani mai shekara 29, Usman Muhammad, bisa laifin yin amfani da hotunan tsiraici yana damfarar maza ta shafukan zumunta.
Ofishin Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) na Ilorin ya maka shi kotu bisa zargin yin basaja a matsayin mace yana yaudarar maza.
“Kai Usman Muhammad, (da aka fi sani da Adepeju Omolara da kuma Guns Omolara Valley), a cikin watan Fabrailu 2020, ka yi kokarin aikata laifin damfarar maza ta hanyar gabatar da kanka a matsayin mace mai suna Omolara Adepeju dan kuma Guns Omolara Valley, kamar yadda tattaunawarka da su a shafukanka na Whatsapp da Facebook ta nuna a cikin wayarka.
“Saboda haka ka aikata laifin da ya saba wa sashen na 95 na dokokin Arewacin Najeriya”, inji jami’in EFCC mai gabatar da kara, Adenike Ayoku,
Ya kuma kuma shaida wa kotun cewa mai laifin na amfani da hotunan tsiraicin mata yana karbar kudi a hannun maza a kafafen sa da zumunta, kamar yadda suka gani a shafukansa na Facebook da WhatsApp.
Matashin ya kuma amsa laifin da aka zarge shi da aikatawa.
Da yake yanke hukunci, Mai shari’a, Sikiru Oyinloye, ya ce ya gamsu da hujjojin da mai gabatar da karar, saboda haka ya umarci Muhammad ya biya tarar N50,000 cikin awa 24 ko ya tafi kurkuku na wata shidda.
Ya kuma ce wayoyin da ya yi amfani da su wajen yin damfarar sun zam a mallakin gwamatin tarayya.