Babbar Kotun Jihar Yobe ta yanke wa Mai Binciken Kudi na Ma’ikatar Kananan Hukumomin Jihar hukuncin daurin shekara biyar a gidan gyaran hali.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Muhammad Lawu Lawan ne dai ya yanke hukuncin ranar Litinin, bayan ya sami Alhaji Idris Yahaya da almundahanar Naira miliyan 19.
- Ba mu muka ce CBN ya bijire wa umarnin Kotun Koli kan canjin kudi ba – Fadar Shugaban Kasa
- Isra’ila ta saki Bafalasdine bayan ya shafe shekara 17 a daure
Ofishin Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC na shiyya da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno ne dai ya gurfanar da wanda ake zargin tun da farko.
Ana zargin Alhaji Idris ya karbi kudaden ne da nufin sayo wasu motoci kirar Toyota Corolla 2015, da za a yi amfani da su a ma’aikatar, amma ya karkatar da su.
An gurfanar da shi ne ranar Laraba, 9 ga watan Nuwamban 2022, inda aka yanke masa hukuncin bayan ya amsa aikata laifin.
Da yake yanke hukuncin, Mai Shari’a Muhammad ya ce masu kara sun gabatar wa kotun gamsassun hujjojin da suka tabbatar da zargin da ake yi wa mutumin.
Daga nan ne ya yanke masa hukuncin daurin shekara biyar tare da zabin biyan tara.
Kazalika, alkalin ya umarci mai laifin ya biya Naira miliyan 10 da dubu 100 ga Gwamnatin Yobe ta hannun EFCC, koya shafe karin wasu shekaru biyu a daure.