✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daure mai amfani da hoton batsa wajan damfara a yanar gizo

Wata babbar kotun Tarayya da ke zama a Abeokuta ta daure wani matashi da ke amfani da hotunan batsa yana yaudarar abokan huddarsa inda yake…

Wata babbar kotun Tarayya da ke zama a Abeokuta ta daure wani matashi da ke amfani da hotunan batsa yana yaudarar abokan huddarsa inda yake damfarar su ta wannan siga.

Jami’an Hukumar yaki da ta’annatin tattalin arzikin kasa ta EFCC shiyar garin Ibadan ne suka shigar da karar matashin mai suna Ahmed Oladimeji, a gaban mai shari’a Wasilat Ibrahim ta babbar kotun wacce ta same shi da laifin aike hotunan batsa ta hanyar na’ura mai kwalkwalwa laifin da ya sabawa sashi na 24 (1)(a) na dokar laifuka a yanar gizo ta shekarar 2015 wacce ke da hukuncinta a karkashin sashi na 24(1)(b) na dokar.

Ahmed Oladimeji ya amsa laifin sa ya nemi afuwa lamarin da ya sanya alkalin ta yi masa sassauci inda aka yi masa daurin watanni hudu na gidan kaso da kuma horon yin aiki a lokacin da yake daure, kana dole ya mayar da kudin kasar waje da ya damfara ga masu shi.

Kotun ta kuma kwace na’ura mai kwalkwaluwa kirar Toshiba da wayar salula ta ifon 6 da ta Tekno KA da aka same shi da su ta kuma mallakawa gwamnatin Tarayya kayayyakin.