✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure ma’aurata kan garkuwa da mai juna biyu

Wata babbar kotun majistare da ke zamanta a birnin Makurdi na Jihar Binuwai ta ba da umarnin tsare wani dan kasuwa mai suna Benjamin Utah…

Wata babbar kotun majistare da ke zamanta a birnin Makurdi na Jihar Binuwai ta ba da umarnin tsare wani dan kasuwa mai suna Benjamin Utah a matarsa Ada a gidan wakafi bisa zargin garkuwa da wata mata mai juna biyu.

Tun da farko dai ‘yan sanda sun zargi ma’auratan da hada baki wajen aikata laifin wanda ya saba da sashe na 97 na kundin Penal Code na Jihar Binuwai na shekara ta 2004.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Vincent Kor ya yi watsi da korafin wadanda ake zargin na cewa kotun ba ta da hurumin sauraron karar, ya kuma dage sauraron shari’ar  zuwa ranar 26 ga watan Oktoba.

Dan sanda mai shigar da kara Insfekta Hyancinth Gbakor ya shaida wa kotun cewa wacce ta ke karar mai suna Isiana Amarach an sace ta ne daga Inugu aka kai ta gidan ma’auratan a Makurdi a ranar daya ga watan Agusta.

Ya kuma shaida wa kotun cewa Ada ta tilasta wa mai juna biyun zama tare da su har sai ta haife abin da ke cikinta.

Dan sandan ya kuma ce matar ta yi alkawarin bai wa ma’auratan Naira dubu 300 idan ta haihu, amma suka yi kememe har ma su ka yi barazanar hallaka ta.

Insifekta Hyancinth ya ce har yanzu ana kan bincike a kan lamarin inda ya bukaci kotun da ta dage sauraron karar.

Daga nan ne lauyan wadanda ake karar, A.A. Andenira ya roki kotun da ta bayar da belin su.

Sai dai a wata takardar tuhumar ta daban a cikin wannan kotun dai, an sake gurfanar da Ada bisa zargin sace jariri mai wata hudu da haihuwa a kasuwar Kadarko ta Jihar Nasarawa.

Ita ma wannan shari’ar an dage ci gaba da sauraronta hai zuwa 26 ga watan Oktoba.