Wata Kotun Majistire da ke zamanta a yankin Ile-Ife na jihar Osun, ta daure wani ma’aikaci sabodar satar kayan da darajarsu ta kai Naira miliyan 1.5 na wani dan kasuwa.
Dan sandan da ya gabatar da kara gaban alkalin kotun, ya bayyana cewar ana tuhumar ma’aikacin da cin amana da sata.
- An kone wanda ake zargi da satar babura kurmus a Osun
- An ba wadanda suka saci kayan tallafin Osun sa’o’i 72 su dawo da su
- Kotu ta tsare matashin da ya daba wa makwabcinsa wuka
James Obaletan ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 15 ga Disamba 2020.
Ya kara da cewa wanda ake zargin ya shiga gidan wani mutum mai suna Abolaji Bukola, inda ya satar masa kayayyaki wanda darajarsu ta kai N1.5m.
A cewarsa laifin ya saba wa sashi na 383, 390 da kuma 412 na kundin laifuka na jihar Osun na shekarar 2002.
Alkalin kotun A.A. Adebayo ya umarci wanda ake zargin da ya nemi lauya don kare sa a gaban kotun.
Kazalika, ya bada umarnin tura wanda ake zargi zuwa gidan maza sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2021.