Wata kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja, ta tabbatar da Sanata Muhammad Danjuma Goje, a matsayin halastaccen ɗan jam’iyyar APC a Jihar Gombe.
Wannan na cikin wani hukunci da kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Abba B. Mohammed, E.O ta yanke.
- Olympics: Rashin shugabanni nagari ya shafe mu — Obi
- Obasanjo bai halarci taron majalisar ƙasa da Tinubu ya kira ba
Alƙalan sun yi watsi da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke, sannan suka umarci APC a Jihar Gombe ta biya tarar Naira 200,000.
A watan Yulin 2023 ne, Sanata Goje, ya shigar da ƙara kan hukuncin da ya tabbatar da korarsa daga shugabannin jam’iyyar APC a gundumar Kashere da ke Ƙaramar hukumar Akko a jihar.
A ranar 4 ga watan Yuli, 2023 ne, Goje ta hannun lauyansa, Paul Erokoro (SAN), ya shigar da ƙara a gaban kotu yana ƙalubalantar korarsa daga jam’iyyar.
Ya shaida wa kotun cewa ƙaramar kotun ta yi kuskure a hukuncin da ta yanke, saboda an tauye masa haƙƙinsa na yin adalci.
A cewar Goje, wasiƙar da Shugaban Gundumar, Tanimu Abdullahi ya rubuta, bai fayyace ayyukan da ake zarginsa aikatawa ba.
Aminiya ta ruwaito yadda jam’iyyar APC ta kori Goje bisa zargin yi wa jam’iyyar zagon ƙasa a zaɓen 2023.