✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure lauyan bogi wata 15 a Kano

Kotu ta daure lauyan bogi wata 15 a Kano

Wata Kotun shariar Musulinci da ke zamanta a Karamar Hukumar Kiru ta Jihar Kano, ta yanke wa wani mutum mai suna Zaharaddin Sani Maidoki hukunci daurin wata 15 a gidan da gyaran hali.

Kotun dai ta samu mutumin, wanda mazaunin Jihar Kaduna ne, da laifin aikata sojan gonar cewar shi lauya ne.

Bayan mai gabatar da kara ya karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa, mutumin ya amsa laifin sa ba tare da ya wahalar da shari’ar ba.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Abdulmuminu Nuhu Gwarzo, ya kafa masa shaidun jin ikirari kan laifin da ya amsa, inda kotun ta yi amfani da dokokin shari’a na Jihar Kano karkashin sashe na 337 na shekarar 2000.

Tun da farko dai Zaharaddin ya yi ikirarin cewa shi lauya ne, daga bisani kuma ya ce shi dan jarida ne daga Jihar Kaduna.

A zaman da ya gabata, kotun ta aike da takaddar gayyata ga Kungiyar Lauyoyi (NBA) ta Jihar Kaduna, inda ta shaida wa kotun cewar mutumin ba mambansu ba ne kuma ba ya cikin kungiyarsu.

Tun da farko, ya bayyana kansa a matsayin lauyan da zai kare wasu mutane da ake zargi da aikata wani laifi.

Mai Shari’a Abdulmuminu Gwarzo ya yanke masa hukuncin daurin shekara daya babu zabin biyan tara, kuma zai biya N20,000. Idan kuma ya gaza biya zai shafe watanni uku a gidan yarin.

Kotun ta kuma kwace littafinsa na rubuce-rubuce da katin shaidar aiki a yayin da mai shari’a ya ce idan bai gamsu da hukuncin ba yana da damar daukaka kara cikin kwana 30.