✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure jarumin Kudancin Najeriya shekara 16

Kotun ta same shi da laifin cin zarafin yarinya

Wata kotu a jihar Legas ta daure fitaccen jarumi a masana’antar Nollywood ta Kudancin Najeriya, Olanrewaju Omiyinka James, wanda aka fi sani da Baba Ijesha shekara 16 a gidan yari.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Oluwatoyin Taiwo ta samu jarumin ne da laifin cin zarafin karamar yarinya mai shekara 16 a tsakanin shekarun 2013-2014.

An kai karar jarumin ne bisa tuhume-tuhume guda shida, inda Alkalin ta tabbatar da guda hudu, ta wanke shi a sauran.

Wannan hukuncin na zuwa kwanaki kadan bayan wata kotu a Amurka ta daure mawakin Amurka, R. Kelly shi ma saboda cin zarafin.