Wata kotun majistare da ke Ilorin a Jihar Kwara, ta ba da umarnin tsare wani Fasto mai suna Makanjuola Olabisi, bisa zargin yi wa wasu ’yan mata uku ’yan uwan juna fyade.
Jami’in dan sanda mai gabatar da kara, Insifekta Matthew Ologbonsaye, ya bayyana wa kotun cewa faston ne ya shawarci ’yan matan da su dinga zuwa ibada cocinsa da ke Agba Dama a Ilorin tun a shekarar 2018.
To sai dai ya yi hakan ne bayan watsi da tayin soyayyarsa da babbar ciki ta yi, wanda ya kai shi ga yi mata fyade da sauran ’yan uwanta da suke uwa daya uba daya a lokuta daban-daban.
Ganin hakan ne ya sanya suka daina zuwa cocin, lamarin da shi kuma ya sanya Faston ya fara yi musu barazana.
Dan sandan ya kuma bukaci kotun da ta ci gaba da tsare Fasto har zuwa lokacin yanke shawarar karshe da Daraktan kula da shigar da kara na ma’aikatar shari’ar jihar zai yi.
Aminiya ta ruwaito Alkaliyar kotun, Fatima Salihu ta ba da umarnin tsare faston a gidan kaso, tare da dage shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Satumbar 2022.