Wata babbar kotu da ke zamanta a yankin Ekot Ekpene na Jihar Akwa Ibom, ta tura wani malamin Jami’ar Calabar, Farfesa Peter Ogban zuwa gidan kaso bayan samunsa da magudin zabe.
Farfesa Ogban shi ne ya yi baturen zabe yayin zaben kujerar majalisar dattawa ta mazabar Arewa maso Yammacin Akwa Ibom a zaben 2019.
- Yadda gasar karatun Al-Kur’ani ta Kasa ke gudana a Kano
- Faransa za ta taimaka wa Najeriya yaki da fashin teku
Hukumar Zabe ta Kasa INEC, wacce ta yi karar Farfesa Ogban, ta yi zarginsa da fitar da bayanai da kuma sanar da sakamakon bogi a Kananan Hukumomin Oruk Anam da Etim Ekpo.
Kotun wacce mai Shari’a Augustine Odokwo ya jagoranci zamanta, ta yanke wa Farfesan hukuncin cin sarka na watanni 36 da kuma biyan tara ta naira dubu dari.
Farfesan masanin kimiyyar kasa ta bakin lauyansa, Anthony Ekpe, ya roki kotun da ta yi masa sassauci bayan zartar da hukunci a kansa.
“Ina da wadanda suka dogaro da ni ciki har da mahaifiyata mai shekara 90 da take bukatar a kula da ita.
“Mutanen yankina suna mutunta ta ni kuma an dauke ni da daraja sosai a Jami’ar da nake karantarwa da ma sauran Jami’o’in Calabar baki daya.”
“Yanzu idan aka toshe min hanyar samun abinci, hakan na nufin dukkan wadanda suka dogara da ni za su tsinci kansu cikin mawuyacin hali,” a cewarsa.
An same shi da laifin sauya sakamakon zaben domin taimaka wa jam’iyyar APC, a lokacin da Ministan Neja Delta na yanzu, Godswill Akpabio ya yi takara a zaben bayan ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP.
Yayin wani zama da aka yi da Farfesan, ya shaida wa kotun yadda aka sauya sakamakon zaben ta yadda APC za ta samu nasara a kan PDP.
Sai dai duk da haka, dan takara na jam’iyyar PDP, Chris Ekpenyong wanda ke zaman tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom, shi ne ya yi nasarar a zaben wanda a wancan lokaci rikici ya mamaye.