Babbar Kotu mai zamanta a Ibadan, babban Jihar Oyo, ta daure wani dillalin tabar wiwi shekara biyu a gidan yari.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Uche Agomoh, ce ta yanke wannan hukunci ranar Juma’a.
- Dokar Cire Kudi: Emefiele Ya Wuce Gona Da Iri —Dan Majalisa
- Kotu ta ba da belin masu barazanar yada hotunan tsiraci
Agomoh ta ce ta daure mai laifin ne bayan da ta gamsu da hujjojin da Hukumar NDLEA, mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, ta gabatar mata.
Ta ce, ta yi na’am da rokon sassaucin da mai laifin ya yi, kasancewar wannan shi ne karon farko da ya aikata makamancinsa.
Tun farko, lauyan NDLEA a jihar, Mista D.O. Otunla ya fada wa kotun cewa an gurfanar da mai laifin ne saboda ta’ammali da miyagun kwayoyi ta haramtacciyar hanya.
Ya ce, NDLEA ta kama shi ne a ranar 1 ga Agusta a yankin Karamar Hukumar Akinyele a jihar.
Otunla ya ce laifin da ya aikata ya saba wa Sashe na 11 (C) na Dokokin NDLEA da Doka mai lamba Cap. No.30 na Dokokin Kasa na 2004.
(NAN).