Babbar Kotun Jihar Kano Mai lamba 5, ta yanke wa wani dan kasuwa hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara biyar ba tare da zabin biyan tara ba, sakamakon samunsa da laifin almundahanar Naira miliyan biyar da rabi.
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ce ta gurfanar da wanda ake zargin mai suna Alhaji Manniru Sagagi a gaban kotun bisa tuhumarsa da laifin hadin baki da cuta inda ya zambaci wani dan kasuwa mai suna Nasiru Abubakar Naira miliyan biyar da rabi inda ya yi masa dadin bakin cewa zai nema masa bashin wasu kudade daga Bababn Bankin Najeriya (CBN).
Wanda ake zargin ya amsa laifinsa wanda ya saba da sashe na 07 na Kundin Shari’ar Manyan Laifuffuka.
Da take yanke hukunci, Alkalin Kotun Mai shari’a Dije Aboki ta daure dan kasuywar shekara biyar a kurkuku ba tare da zabin biyan tara ba. Kuma ta ce mai laifin zai biya dan kasuwar kudinsa Naira miliyan biyar da rabi.