✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure barawon babur wata 9 a gidan yari

Shi da abokansa suka sace babur din bayan mai shi ya faka a kofar gida

Wata kotun shari’ar Musulinci da ke zamanta a Kano ta yanke hukunci daurin wata tara a gidan yari kan laifin satar babur mai kafa biyu.

An gurfanar da matashin ne tare da wasu abokansa uku da suka gudu, bisa zargin hada kai da aikaita sata, bayan da mai babur din, Mustapha Jafar Tudunwada, ya faka shi a kofar gida.

An kiyasta kimar kudin babur din mai launin baki kirar Companion ya kai Naira dubu 240.

A zaman kotun na ranar Laraba, mai gabatar da kara, Aliyu Abidin Murtala ya karanto wa matashin zargi kunshin tuhumar da ake yi masa, ya kuma amsa cewa shi ya saci baburin din tare da wasu abokansa.

Daga nan Mai Shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmad ya yanke masa hukuncin daurin wata 9 a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya tare da biyan kudin rankon naira dubu 240 ga mai kara.