✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta raba auren shekara 14 saboda zargin cin amana

Wata kotun al’ada dake zamanta a Ibadan babban birnin jihar Oyo ta datse igiyar wani aure mai kimanin shekaru 14

Wata kotun al’ada dake zamanta a Ibadan babban birnin jihar Oyo ta datse igiyar wani aure mai kimanin shekaru 14 tsakanin wani dan kasuwa, Yakeen Afeez da matarsa mai suna Sekinat bisa zargin cin amana da rashin girmama juna.

Da yake yanke hukuncin, babban alkalin kotun, mai shari’a Ademola Odunade ya ce ba za a sami zaman lafiya ba idan daya daga cikin ma’aurata ya kasance mai kunnen kashi.

Dagan an sai ya umarci matar da ta ci gaba da kula da ‘ya’ya ukun da suka haifa tare da umartar mijin da ya rika biyan N15,000 kowanne wata a matsayin kudin kula da yaran.

Tun da farko dai Yakeen ne ya roki kotun da ta kashe auren bisa zargin da ya yi wa matar tasa da yin yin mu’amala da wasu mazan da kuma yin gararanba a gari, duk kuwa da cewa ta san tana da aure.

Ya ce, “Ba ta yi wa yaran girki ko kadan. Na kuma sha kamata a yanayi mara kyan gani da ita da saurayinta, inda shi kuma yake barazanar cutar da ni in har na yi yunkurin daukar wani mataki.

“Wannan matar kunnen kashi ne da ita,  sam ba ta girmama ni, ballanatana dangi na ko iyaye na.

Sai dai Sekinat ta yi na’am da hukuncin kotun na datse igiyar auren.

“Afeez ya kan yi min abubuwan da ba su kamata ba, kuma yana kokarin ya zuba min guba. Kishinsa ya yi yawa,” inji Sekinat.