Kotun Ma’aikata ta dage karar da Gwamnatin Tarayya ta shigar gabanta, tana neman a tilasta Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU), janye yajin aikin da ta shafe watanni bakwai tana yi.
Alkalin kotun P.I Hamman ya dage shari’ar zuwa ranar 16 ga watan Satumba.
- Wata mata ta kashe kanta saboda nauyin bashi
- Sun yi garkuwa da jariri, suna dukan mai jego don a ba su N50m
A zaman kotun na ranar Litinin ne dai Kungiyar SERAP ta roki shiga shari’ar.
Lauyan kungiyar, Ebun-Olu Adegboruwa ya ce wadanda ya ke wakilta sun shigar da makamanciyar karar, inda suka bukaci kotun ta tilasta Gwamnatin Tarayya cika alkawuran da ta daukarwa ASUUn a shekarar 2009.
“Mun shigar da makamanciyar wannan karar a ranar 8 ga Satumba, inda muke bukatar kotun ta tilastawa Gwamnati cika alkawuran da ta daukarwa ASUU”, in ji Lauyan.
A don haka ya ce kungiyar na son shiga shari’ar, don kar ayi shari’a biyu kan mas’ala daya.
Sai dai lauyan Gwamnati, Tijjani Gazali ya soki wannan bukata a Lauyan SERAP, in da ya sanar da Alkalin cewa kungiyar ta yi riga malam masallaci, kasancewar ranar Litinin aka fara zaman shari’ar.
Da yake yanke hukunci kan bukatar SERAP, Alkalin ya amince da bukatar Gwamnatin yana mai cewa shari’ar ba ta yi kwarin da za a yi mata hadin gwiwa ba.
Haka kuma Hamman ya ce yana sauraron karar ne a madadin wani Alkali da a yanzu ya ke hutu, don haka akwai yiwuwar wani Alkalin ne zai ci gaba da sauraron shari’ar a gaba.
Kazalika, alkalin ya shawarci Gwamnatin da ASUUn har ma da SERAP, da su yi musayar rubuce-rubucen da suka gabatar a gabanta, kafin ranar 16 ga Satumba da za a ci gaba da sauraron karar.