✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ci tarar Gwamnatin Kano saboda rushe gine-gine 

Muna nazari kan hukuncin da kotun ta yanke gabanin daukar matakin da ya dace.

Wata Babbar Kotun Tarayya ta bai wa Gwamnatin Kano umarnin biyan tarar naira miliyan biyu saboda yunkurin rushe wa wasu gine-gine.

Kotun dai ta umarci Gwamnatin Kano da ta biya wasu mutum biyu naira miliyan daya-daya saboda yunkurin rushe gine-ginensu a Unguwar Salanta da ke jihar.

Alkalin da ya jagoranci zaman kotun a wannan Juma’ar, Mai Shari’a Simon Amobeda, ya ce Gwamnatin Kanon ta sauka daga kan turba ta daidai saboda shafa wa gine-ginen nasu fenti mai nuna alamar rusau zai biyo ta kansu kan zargin an yi su ne ba bisa ka’ida ba.

Mai Shari’a Simon ya kafa hujjar cewa, Gwamnatin ta saba wa sashe na 43 da 44 da ya bai wa wadanda abin ya shafa — Saminu Shehu Muhd da Tasiu Shehu Muhammad — ’yancin mallakar gine-gine kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanadar.

Aminiya ta ruwaito cewa, gine-gine da lamarin ya shafa sun hada da fulotai masu lamba 41 da 43 da kuma 68 a Unguwar Salanta.

Kazalika, kotun ta riki cewa kutse da Gwamnatin Kanon ta yi a gine-ginen da misalin karfe 11 na daren ranar 14 ga watan Yunin 2023 ya saba wa tanadin Kundin Tsarin Mulkin na Kasa.

Kotun ta kuma bai wa Gwamnatin Kano umarnin sake fentin gine-ginen wanda Hukumar Tsara Birni ta Kano KNUPDA ta shafa wa alamar mai dauke jan fenti.

Da yake batu bayan hukuncin, Barista Bashir Ibrahim wanda ya shigar da kara a gaban kuliya, ya bayyana hukuncin da kotun ta yanke a matsayin abun yabawa saboda kare ’yanci da martabar bilAdama.

A nasa bangaren, Lauyan Gwamnatin Kano, Barista Musa Dahuru Muhad, ya ce za su yi nazari kan hukuncin da kotun ta yanke gabanin daukar matakin da ya dace.