Alkalin kotun, Mai Shari’a Zainab Abubakar ta ce wadanda za su biya diyyar ga dan kasuwar sun hada da Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya.
- Karin kudin data da kiran waya na nan daram —Gwamnatin Tarayya
- Fafaroma Bai Hana Ni Yi Wa Musulmi Yakin Neman Zabe Ba —Lalong
Ta kuma bayyana cewa haramtacce ne abin ’yan sanda suka yi na tsare dan kasuwar mai suna Victor Ojionu ba tare da izini ba.
Sannan ta umarci kafofin yada labarai na na Naijaloaded, Instablog, Legit.ng, Vanguard, and the Guardian da su janye labaran da suka wallafa game da zargin dan kasuwan.
Alkalin yanke hukuncin ne bayan Mista Ojionu ya shigar ga kara kan baje-kolinsa da ’yan sanda suka yi a gaban ’yan jarida a matsayin wanda ake zargi.
Mutumin ya shigar da karar ne bayan a ranar 17 ga Satumban 2019 ’yan sanda sun tsare dan kasuwar tare da gabatar da shi gaban ’yan jarida a matsayin wanda ake zargi.
Lauyansa, Marshal Abubakar ya bayyana wa kotu cewa sanya masa ankwa da gabatar da shi a gaban ’yan jarida ya zubar masa da kima da kuma tauye hakkinsa na dan Adam kamar yadda kundin tsarin mulkin Naejriya da yarjejeniyar kare hakkin bil Adama suka tanadar.