A ranar Larabar da ta gabata ce Kotun Shari’ar Musulunci ta 3 da ke kofar Kudu a birnin Kano ta umarci Maryam Jalal ta biya mijinta Abba Muhammad Tahir Naira miliyan biyar a matsayin kudin khul’i sakamakon kin amincewa ta yi zaman aure da shi.
Abba Muhamamd Tahir ya yi karar matarsa Maryam a kotun ne yana ta tilasta matar tasa ta koma gidansa ko ta biya shi Naira miliyan tara da ya kashe lokacin aurenta.
Da yake yanke hukuncin a kan karar, Alkalin Kotun Mai shari’a Ibrahim Sani Sarki Yola ya ce kotun ta yi hukuncin ne bisa adalci lura da cewa mijin ya yi zaman aure da ita na wata shida har ta samu ciki ya zube, don haka ba za ta biya shi gaba dayan kudin da ya nema ba, kamar yadda kotun ta ki amincewa da Naira dubu 100 da Maryam ta ce za ta biya mijinta domin shi ne sadakin da ta san ya biya. Kotun ta kafa hujja cewa duk abin da aka ce idan babu shi aure ba zai yiwu ba, to shi ma ya zama a cikin sadakin, domin hujjoji sun nuna cewa iyayen Maryam ne suka gaya wa mijinta Muhammad Tahir cewa sai ya biya wadancan kudi kafin auren ya kullu.
A cewar Alkalin, zaman aurensu bai yi karkon da za a ce matar ta ci wannan makudan kudi da mijin ya kashe a lokacin auren ba.
Alkalin ya cewa kotu ta yi watsi da bukatar mai kara da nemi matar ta biya shi kudin da ya kashe na kama mata gidan zama, inda Alkalin ya ce dama yana cikin hakkin miji ya tanadar wa matarsa wurin zama.
Kuma kotun ta yi watsi da bukatar wacce ake kara cewa mijin ya biya ta Naira miliyan uku kudin abincinta da na magani da ta kashe a tsawon shekara uku da rabi da ta zauna a gidansu tunda tana matsayin matarsa, inda Alkalin ya ce ba da izinin mijin ta tafi gidansu ba kuma hujjoji sun nuna cewa ya yi bakin kokarinsa ta koma dakinta amma ta ki. Alkalin ya ce idan wacce ake kara ba ta gamsu da hukuncin kotun ba za ta iya daukaka kara zuwa kotun gaba cikin kwana 30 daga ranar yanke hukuncin.
Lauyan mai kara Barista Muhammad Iliyas ya bayyana wa Aminiya farin cikinsa da gamsuwa da hukuncin duk da ba su samu kudin da suka nema ba. “A shirye muke mu je duk kotun da suka daukaka kara zuwa gare ta, watakila ma mu samu kudin da muka nema ya fito gaba daya. Muna so jama’a su fahimci cewa wannan mata ta saba yin hakan, domin a gabanku ’yan jarida wani lauya ya tashi ya bayyana wa alkalin cewa a aurenta na farko mijin ya kashe mata kimanin Naira miliyan 20, amma bayan watanni da auren sai ta ki zama a gidansa. Da ya kai kotu aka fara shari’a sai ya janye ya kuma yafe mata kudin. To mu ba za mu yafe ba, domin muna so abin ya zama darasi a kanta da iyayenta da sauran masu irin wannan hali,” inji Lauyan.