✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ce INEC ta ba Atiku damar duba kayan zabe

Kotun Sauraron Karar Zaben Shugaba Kasa ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta  ba dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar…

Kotun Sauraron Karar Zaben Shugaba Kasa ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta  ba dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar damar duba kayayyakin zaben da aka yi amfani da su a zaben Shugaban Kasa na ranar 23 ga watan Fabrairu.

Kotun mai alkalai uku a karkashin jagorancin Mai shari’a Abdul Aboki ta yanke wannan hukunci ne a Abuja a shekaranjiya Laraba. Sauran wakilan kotun su ne Mai shari’a Emmanuel Akomaye da Peter Ige.

Lauyoyin Atiku da Jam’iyyar PDP Lebi Uzoukwu (SAN) da Chris Uche (SAN) ne suka bukaci haka daga kotun zaben.

Lauyoyin sun bukaci kotun ta umarci Hukumar INEC ta ba su  rajistar masu zabe da na’uroin tantance masu zabe da takardun kada kuri’a da sauran muhimman kayayyakin zaben da aka yi amfani da su a zaben na Shugaban Kasa domin su duba su, sannan su dauki hotunansu.

Amma sai kotun ta ki amincewa da bukatar kididdigar daukar hoton kayayyakin zaben.

A hukuncin da ta yanke, kotun ta ce sashe na 151, sakin layi na 1 da na 2 na Dokar Zabe ya amince Hukumar  INEC ta ba wanda yake bukata damar duba kayayyakin zabe amma ban da  daukar hoto, inda ta kara da cewa ba za yi amfani da hotuna ba a matsayin shaida.

Sannan kotun ta ce masu karar za su yi amfani ne da kayayyakin da suka  duba kuma suka fito daga Hukumar INEC.

A makon jiya ne Hukumar INEC ta bayyana Shugaba Buhari na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya doke abokin karawarsa na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar, inda Shugaba Buhari ya samu kuri’a miliyan 15 da dubu 191 da 847, Atiku ya samu kuri’a miliyan 11 da dubu 262 da 978. Atiku ya yi watsi da sakamakon zaben, inda ya sha alwashin zuwa kotu.

Tuni dai APC ta ce a shirye take ta hadu da PDP da dan takararta a kotun.

Daraktan Watsa Labarai na Yakin Zaben Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC, Festus Keyamo (SAN) ya ce Atiku Abubakar yana da damar zuwa kotu domin kalubalantar sakamakon zaben.

“Shigar da kara kotu domin nuna rashin amincewa da sakamakon zabe ita ce hanya mafi dacewa a siyasance, don haka hana mutum zuwa kotu kamar danne masa hakkinsa ne. Don haka a shirye muke mu hadu da Atiku Abubakar a kotu domin mu nuna wa duniya cewa lallai an gudanar da zabe mai inganci, kuma an kada shi,” inji shi.

Keyamo ya kara da cewa, “Ba zai yiwu a ce an yi magudin zabe kawai don wanda ya sha kaye ya fadi haka ba. Abin da Atiku da PDP suke yi ke nan. Sai dai kuma inda suka yi rashin sa’a shi ne yadda masu lura da zabe na duniya suka bayyana zaben a matsayin mai aminci da nagarta.”