✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta bayar da belin Mahdi Shehu

Wata babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta bayar da belin Mahdi Shehu kan kudi N10m. Kotun karkashin jagorancin Mai shari’a Louis Alagoa,…

Wata babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta bayar da belin Mahdi Shehu kan kudi N10m.

Kotun karkashin jagorancin Mai shari’a Louis Alagoa, ta amince tare da bayar da belin yayin zamanta na ranar Alhamis.

Sai dai kotun ta gindaya masa sharadin kawo mutum daya da zai tsaya masa wanda mallaki kadarar da ta kai darajar naira miliyan 10 sannan kuma dole ta ya kasance a Kano.

Kotun ta ce za a ci gaba da tsare har sai ya cika sharduddan da gindaya masa inda kuma dage sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Mayun 2021.

Idan ba a manta ba gwamnatin jihar Katsina ce ta shigar da karar Mahdi Shehu dangane da wasu bayanai da ya bayar na zargintada badakala cin hanci da rashawa.