Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis ta bayar da belin dakataccen Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda, DCP Abba Kyari.
Kyari dai ya kasance a tsare tun lokacin da aka kama shi a shekara ta 2022.
- Tinubu ne da kansa zai bayyana sabuwar ranar da za a yi kidayar jama’a – NPC
- INEC ta maka wanda ya ce Binani ce ta lashe zaben Gwamnan Adamawa a kotu
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ce ta gurfanar da shi kan zarginsa da hannu a wata badakalar Hodar Iblis da nauyinta ya kai kilogiram 25.
Daga bisani ne aka kama shi sannan aka gurfanar da shi a gaban kotu, wacce kuma ta bayar da umarnin garkame shi a kurkukun kuje da ke Abuja.
Rundunar ’Yan sanda ta Kasa dai ta kafa wani kwamiti da zai bincike zargin rashin da’ar da ake yi wa Abba Kyari, wanda shi ne tsohon Shugaban rusasshen Sashen Leken Asiri na Rundunar (IRT).
Daha bisani kuma an dakatar da shi daga aikin na dan sanda gaba daya.
A ranar Alhamis, alkalin kotu, Mai Shari’a Kolawole Omotosho, ta bayar da belin nasa bisa tsauraran sharuda.
To sai dai har yanzu yana fuskanta wata tuhumar aikata laifi a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite, ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.