Wata Kotun Majistare da ke Gyadi-Gyadi a Jihar Kano, ta bayar da belin ɗan jaridar nan da ake zargi da wallafa wasu faifan bidiyo na sukar wani hadimin gwamnan jihar.
Tun da farko ’yan sanda sun kama ɗan jaridar mai suna, Mukhtar Dahiru, wanda ma’aikacin gidan rediyon Pyramid FM ne da ke Kano.
- Ƙara Farashin Mai: Yadda Tinubu ya yaudare mu — NLC
- An yi jana’izar mutum 34 da Boko Haram ta kashe a Yobe
Kotun, ta bayar da belin ɗan jaridar kan kudi Naira miliyan ɗaya.
Haka kuma kotun ta shimfida masa sharuɗan belin, ta hanyar samar sa shugaban ƙungiyar ’yan jarida ta Jihar Kano da matarsa da kuma wani mutum daban wanda ya samu sahalewar Hukumar Hisbah.
Idan za a iya tunawa ana tuhumar ɗan jaridar kan ƙarar da mashawarcin Gwamnan Kano, kan harkokin siyasa, Anas Abba Dala ya yi.
Hadimin, ya yi zargin cewa Mukhtar ya wallafa a shafinsa cewa shi jahili ne, tare da ɓata masa suna ta hanyar masa ƙage.
Har wa yau, an zargi ɗan jaridar da ɗora wasu bidiyon a shafinsa na Facebook kan zargin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da cin hanci da rashawa.
Ɗan jaridar ya wallafa wani sautin murya da wani ɗan adawa, ya zargi Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, cewa yana yaudarar mutane da sunan tausaya musu bayan ya kasance almubazzari.
Kazalika, an ruwaito cewar ya wallafa cewar hadimin gwamnan, ya yi zargin cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ba asalin ɗan Najeriya ba ne.
Sai dai ɗan jaridar, ya musanta laifukan da ake zarginsa na haɗa baki da ɓata suna da kuma zagi.
Laifukan dai sun saɓa da sashe na 97 da 391 da 115 na Kundin Pinal Kod.
Mai gabatar da ƙara, lauyan Gwamnati Barista Safiya Yahaya, ta ce ba su da suka game da belin da aka bayar duba da cewa laifukan da ake zargin ɗan jaridar laifuka ne da za a iya bayar da beli a kansu.
Barista Dahiru Yahuza, wanda shi ne lauyan wanda ake ƙara ya bayyana jin daɗinsu game da belin da kotun ta ba su.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Umma Kurawa, ta bai wa ɗan jaridar umarnin ya nesanta kansa da wallafa wasu munanan kalamai da za su taɓa mutuncin mai ƙara a shafukansa na sada zumunta.
Ta ɗage shari’ar zuwa ranar 2 ga watan Oktoba, 2024.