Wata Babbar Kotu a Ikeja da ke Jihar Legas ta bayar da umarnin ci gaba da tsare tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.
Za a ci gaba da tsare Emefiele a hannun hukumar EFCC mai yaƙi da yi wa arzikin Najeriya zagon ƙasa har zuwa ranar 11 ga watan Afrilu da kotu za ta yanke hukunci kan ba shi beli.
Mai shari’a Rahman Oshodi ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi kan zargin amfani da ofishinsa ba bisa ka’ida ba da kuma badaƙalar dala biliyan 5.5 da Naira Biliyan 2.8 da ake yi masa.
Alkalin ya ba da umarnin a tsare Henry Isioma-Omoile, wani da ake zargi da hannu wurin taimaka wa Emefiele ya yi barna a gidan yari na Ikoyi.
Lauyan wanda ake kara, Mista A. Labi-Lawal, ya buƙaci kotun da ta bayar da belin waɗanda ake kara la’akari da matsayinsu.
Labi-Lawal, ya ce wanda ake kara na farko (Emefiele) ya yi biyayya ga dokokin belin da mai shari’a Muazu ya ba shi a shari’ar da ake yi masa kan zambo cikin aminci a Abuja.
Ya ce tuhume-tuhumen da ake yi wa Emefile, sun kasance waɗanda za a iya bayar da belinsa saboda ba wani babban laifi ba ne da za a ce babu beli.
“Yanzu muna neman beli ne bisa la’akari da wanda ake ƙara kuma a shirye yake ya riƙa zuwa kotu a duk lokacin da ake bukata.”
“Ya kamata kuma kotu ta yi la’akari da matsayin wanda ake ƙara, a matsayinsa na tsohon gwamnan CBN na kasar.”
Lauyan wanda ake ƙarar ya ce wanda yake karewa yana gabatar da kansa a gaban Mai Shari’a Muazu a Abuja domin ya amsa tuhumar da ake yi masa duk lokacin da aka neme shi.
A cewarsa, wanda ake kara na farko (Emefiele) ba mutum ba ne mai rigima ba, domin shi ne mutum na farko da ya fara zuwa kotu.
Emefiele da wanda ake tuhuman sun ki amsa laifuka 26 da aka karanto musu da suka haɗa da taka ka’idar aiki da karɓar rashawa da karɓar kyaututtuka ta hanyar wakilansu da kuma almundahana, da kuma zamba cikin aminci.
Sai dai lauyan EFCC, Mista Rotimi Oyedepo (SAN), bai nuna rashin gamsuwa da buƙatar neman belin da lauyan Emefiele ya gabatar ba.
Oyedepo ya buƙaci kotu ta yi amfani da hikimarta wurin yanke duk hukuncin da take ganin ya dace kan batun belin.
NAN