✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta bai wa Abba Kyari damar halartar ta’aziyyar mahaifiyarsa

Abba Kyari zai shaƙi iskar ’yanci bayan shafe watanni 27 yana tsare kan badaƙalar hodar iblis.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bayar da belin tsohon kwamandan rundunar leken asiri ta ’yan sandan Nijeriya, DCP Abba Kyari bayan shafe watanni 27 yana tsare.

Da wannan dama ta belin makonni biyu da kotun ta bai wa tsohon jajirtaccen ɗan sandan, zai halarci zaman makokin mahaifiyarsa, Yachilla Kyari da ta riga mu gidan gaskiya a bayan nan.

Kotun ta kuma sanya Juma’a, 31 ga watan Mayu domin nazari kan buƙatar neman beli da ya gabatar a tuhumar laifin fataucin miyagun ƙwayoyi da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta gabatar tun bayan fiye da shekaru biyu da shigarsa hannu a ranar 14 ga watan Fabarairun 2022.

Ana iya tuna cewa, a ranar Lahadi, 5 ga watan Mayun 2024 ne mahaifiyar Abba Kyari ta riga mu gidan gaskiya.

Yachilla Kyari ta rasu ta bar ’ya’ya 10 — da suka haɗa da maza biyar da mata biyar — wanda Abba Kyari ne babban ɗanta.

A shekarar 2022, hukumar ’yan sandan Nijeriya ta dakatar da Kyari da wasu manyan jami’an ’yan sanda biyu — Sunday Ubua da James Bawa — kan zargin hannunsu a hada-hadar hodar iblis da ta shafi mataimakin kwamishinan ’yan sandan da aka dakatar.

Daga bisani kuma hukumar ta NDLEA ta bayyana neman Abba Kyari ruwa a jallo bisa zargin alaƙarsa da wata ƙungiyar masu safarar miyagun kwayoyi ta kasa da kasa.

Tun a wancan lokaci, mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babalola, ya bayyana cewa Abba Kyari da tawagarsa sun wawure kilo 15 daga cikin 25 na hodar iblis da suka kwace a hannun wasu baƙi da suka shigo Nijeriya daga Habasha.