Wata kotu ta umarci wasu da ake zargi da maita da su warkar da wata yarinya mai shekara uku da suka kama.
Kotun Majistare da ke Yola, Jihar Adamawa, ta ba wadanda ake zargin awa 24 su tabbata sun cire bakuwar cutar mai barazana ga rayuwar yarinyar da suka sihirce.
- Na yi wa mata 50 fyade da fashi a gidaje 100
- Kotu ta kwace kudaden tsohon Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari
- ‘Duk wanda aka yi wa lambar NIN kafin 2012 sai ya sake‘
Mai Shari’a Umar Gangs ya ba da umarnin ne a zaman kotun na ranar Litinin bayan wata tsohuwa mai shekara 60 da ake zargi tare da wasu kananan yara biyu sun shaida masa cewa su ne suka da sa wa yarinyar cutar.
An gurfanar da tsohuwar da kananan yaran duk da aka kama su a garin Dumne na Karamar Hukumar Song ne bisa zargin sanya wa yarinyar cutar.
Tsohuwar da yaran suk kuma shaida wa kotun cewa sun kashe mutum bakwai a cikin shekaru bakwai daga lokacin da suka shiga kungiyar maita a garin na Dumne.
Yayin da suke amsa cewa su ne suka jefi yarinyar da cutar, mutanen sun yi ta zargin juna da wasu ’yan uwansu da shigar da su kungiyar maita.
Sun shaida wa kotun cewa sun yi iya kokarinsu na warware maitar da suka jefi yarinyar da ita amma sun kasa; kuma wata mai suna Dudu da yanzu ta tsere ce kadai za ta iya warware sihirin.
Mai Shari’ar, Gangs ya ba da umarnin a kamo ita Dudun nan take, sannan ya ce kotun za ta kama su da laifi idan lafiyar yarinyar ya tabarbare.
Ya yi mamakin ganin kananan yaran da ake zargi maita, ya kuma ce sun yi kankanta a tsare su a gidan gyara hali ko gidan kangararrun yara.