Kotun Majistare mai lamba 12 da ke Gidan Murtala a Jihar Kano ta bayar da umarnin tsare wanda ake zargi da kisan Hanifa Abubakar, Abdulmalik Tanko, a gidan gyaran hali har na tsawon mako biyu.
An dai gurfanar da Abdulmalik tare da wasu mutum biyu ne bisan zargin kisan dalibar, mai kimanin shekara biyar.
- Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 9 a tsakanin Kano da Jigawa
- Barayi sun fasa gidan Benzema lokacin da Madrid ke wasa
Tunda farko mai gabatar da kara Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Musa Abdullahi Lawan ya shaida wa kotun cewa an gurfanar da Abdulmalik Tanko dan kimanin shekaru 34 da Hashim Isyaku dan kimanin shekaru 37 da Fatima Jibril bisa zarginsu da aikata laifuka guda hudu.
Laifukan da ake zargin nasu da sun shafi sacewa tare da boye ta a daidai lokacin da take dawowa daga Makarantar Islamiyya.
Barista M A. Lawan ya kara da cewa “Bayan da ya sace ta ya nemi kudin fansa Naira miliyan shida.
Daga bisani dai alkalin kotun, Mai Shari’a Muhammad Jibril ya dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar biyu ga watan Fabrairun 2022.