Kotun Koli ta Afirka ta Kudu ta bayar da umarnin a mayar da tsohon Shugaban Kasar, Jacob Zuma gidan yari.
BBC ya ruwaito kotun ta kafa hujjar cewa hukuncin da aka yi a bara na sakinsa bisa dalilai na rashin lafiya ya saba wa doka.
Sai dai babu tabbas kan ko zai kwashe wani lokaci a gidan yarin.
A shekarar 2021 ce aka yanke wa tsohon Shugaban Kasar hukuncin dauri na wata 15 bisa kama shi da laifin kin girmama kotu game da binciken da ake yi masa kan zargin rashawa.
Hukuncin daurin da aka yanke masa ya haifar da jerin zanga-zanga a lardin KwaZulu Natal da wasu yankunan kasar.
Sai dai an saki Zuma daga gidan yari cikin wata biyu, bayan da lauyoyinsa suka ce yana fama da rashin lafiya mai tsanani.
A hukuncin da suka yanke ranar Litinin, alƙalan kotun biyu sun bai wa jami’an fursuna na kasar damar yanke hukunci kan za a kirga lokacin da tsohon Shugaban Kasar ya kwashe a waje, a cikin lokacin da ya kamata ya yi a tsare.