Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku a kan kuɗi Naira miliyan 150.
Da yake yanke hukunci, Mai Shari’a Sylvanus Chinedu Oriji ya kuma umurci tsohon gwamnan da ya gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa a matsayin sharaɗin samun belin.
- Adadin waɗanda suka mutu a haɗarin kwale-kwalen Neja ya ƙaru zuwa 24
- Kotu ta yi sammacin Yahaya Bello
An gurfanar da Ishaku ne a gaban ƙuliya tare da tsohon Babban Sakataren Ofishin Kula kula da Ƙananan Hukumomi da Masarautu, Bello Yero bisa tuhume-tuhume 15 da suka haɗa da zagon ƙasa, haɗa baki da kuma wawushe dukiyar gwamnati har Naira biliyan 27.
Alƙalin kotun ya kuma ba da umarnin cewa waɗanda za su tsaya masa dole ne su kasance ma’aikatan Gwamnatin Tarayya kuma a cikinsu ɗaya ya zama ya kai matsayin Darakta.
Hakazalika, ya ce dole ne mutum biyun da za su tsaya su zama mazauna babban birnin tarayya Abuja tare da adiresoshin gidansu wanda magatakardan kotun ya tantance su.
Alƙalin kotun ya hana Ishaku da wanda ake ƙararsu tare fita ƙasar waje ba tare da izinin kotu ba.
Kotun ta bayar da wannan umarni ne bayan lauyoyin da suke kare wanda ake ƙara, Paul Haris Ogbole, (SAN) da Oluwa Damilola Kayode, waɗanda ke wakiltar Ishaku da Yero, duk sun gabatar da buƙatar belinsu ta hanyar furta kalamai da baki, inda suka sanar da kotun cewa an bayar da belinsu.
Lauyan da ke wakiltar Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), Rotimi Jacobs (SAN) bai yi adawa da buƙatar belin tsohon gwamnan ba, bayan da a baya ya dage kan neman a ba da umarnin a hukumance maimakon furtawa da baki.