Kotu ta ba da belin mutumin da ake zargi da yin luwadi da karamin yaro mai shekara bakwai.
Matashi mai shekara 47 da ake zargi da yin lalata da karamin yaron ya samu beli bayan ya shafe shekara biyu a tsare a kurkuku.
Wata Babbar Kotu da ke Kano ce ta ba da belin wanda ake zargin a zamanta na ranar Talata.
An fara gurfanar da wanda ake zargin ne a wata kotun Magistare da ke Gwammaja a Karamar Hukumar Dala a shekarar 2018.
Ana zargin bayan da ya yaudari yaron, mutumin ya cire masa wando ya tura azzakarinsa a duburar yaron har sai da ya yi inzali, wanda ya yi illa ga lafiyar yaron.
A ranar da abin ya faru ne mahaifin yaron ya kai kara ofishin ‘yan sanda da ke tashar Bachirawa inda kama mutumin aka aka gurfanar da shi a kotu.
Lauyar wanda ake tuhuma, Barista Hafsat Sani Kabara ta ce an mayar da karar zuwa Babbar Kotun ne saboda rashin ikon Kotun Magistare na ba da beli kan laifukan manyan laifuka, fyade da laifukan da ba na al’ada ba.
Alkalin da ya sauraran shari’ar, Mai Shari’a Nura Sagir Umar ya bayar da belin wanda ake tuhumar a kan N200,000 sannan ya kawo mutum biyu masu gidaje a unguwar kuma su yi rantsuwar tsaya masa.