✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ba da belin Emefiele a kan N20m

Emefiele ya kalubanci hukumar DSS ta kawo hujjojin da ke tabbatar da zargin da take masa...

Babbar Kotun Tarayya ta ba da belin dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Goodwin Emefiele, a kan Naira miliyan 20.

Mai Shari’a Nichola Oweibi na kotun da ke zamanta a Legas ne ya ba da belin a safiyar Talata, bayan da Emefiele ya musanta zargin da hukumar tsaro ta DSS take masa na mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

A yayin zaman wanda shi ne na farko tun bayan da hukumar ta tsare shi na tsawon kimamin wata guda, Mista Emefiele ya kalubanci ta kawo hujjojin da ke tabbatar da zargin da take masa na mallakar haramtattun makaman.

Bayan musanta zargin ne ya bukaci kotun ta ba da belin sa, kuma alkalin ya amince, bisa da sharadin biyan Naira miliyan 20 da kuma kawo jami’an gwamnati biyu da suka kai matakin albashi na 16 su tsaya masa, su kuma mika wa kotu takardun fasfo dinsu.

Gwamnatin Tarayya ta hannun hukumar DSS ce ta gurfanar da dakataccen gwamnan na CBN a gaban kotun a cikin tsauraran matakan tsaro, kan laifuka biyu — na hada mallakar  bindiga kirar Single-barrel guda daya da kuma albarusai guda 123, ba tare da izinin ba, wanda hakan ya saba wa doka.

Karon farko ke nan da DSS ta gurfanar da shi tun kimanin wata guda da ta fara tsare shi jim kadan bayan hugaban Kasa Ahmed Bola Tinubu ya dakatar da shi daga mukaminsa.