✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta amince da rufe asusun ajiyar Benuwe da EFCC ta yi

Babbar kotun tarayya ta Abuja ta amince da karar da gwamnatin jihar Benue ta shigar akan kalubalantar Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin…

Babbar kotun tarayya ta Abuja ta amince da karar da gwamnatin jihar Benue ta shigar akan kalubalantar Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati EFCC ta shigar don binciken hadahadar kudaden gwamnatin jihar.

Alkali Nnamdi Dimgba ya ce, Hukumar EFCC nada hurumin binciken duk wani abu dake da alaka da tattalin arziki kasa da kuma dukiyar kasa.

A wannan harkar bincike ba bu wanda yake da wata alfarma Gwamna ko mataimakinsa kamar yadda dokar Najeriya ta 1999 sashi na 308 ya tanadar.